Mata sunfi Maza rikon amana, na tabbata bazasu hada kai don a kifar damu ba – Ganduje.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Mata sunfi Maza amana kuma yanada tabbacin bazasu ci amanar gwamnatinshi ba.

Ganduje ya bayyana haka ne, yau Lahadi a fadar gwamnatin Kano a dai dai lokacin da yake raba takardun aiki ga sabbin manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Kano.

“Ba’a taba gwamnati a jihar Kano da ta bawa mata mukamin sakatarorin ma’aikatar gwamnati guda 11 ba sai wannan gwamnatin tamu.”

“Bance Maza basu da amana ba, amma Mata sunfi Maza rikon amana, kuma na tabbata bazasu hada kai dan a kori gwamnati mai ci ba.”

Ganduje ya bayyana sunaye sabbin sakatarorin tare da umarnin fara aiki a gobe Litinin.

Ya bayyana aikin a matsayin na wucin gadi, wanda dukkaninsu zai samu wa’adin watanni uku domin nuna a ga kamun ludayinsu tare da ‘yar jarrabawa.

Gwamnan yace ya aike sunayensu hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi “NDLEA” domin bincikar wadanda basa ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“Mun aike sunayenku ga NDLEA domin a bincike ku, bazamu yadda mu bawa wanda ake ganinshi mutum amma ba mutum ba.”

Gwamnan yace dole ne su kula da ma’aikatun su tare da kula da kuma tafiyar da shugabanci mai inganci.

“Dole ne ku kula da kudaden shiga, Zuwa wajen aiki a kan lokaci, dole a zamana ana aikin zamani da amfani da kwamfuta, dole a zamana an iya rubutu.”

Ganduje yace lallai ne a kula da bandakuna da ofisosin dukkanin ma’aikatun.

“Ina taya ku murna, gobe ne zaku fara aiki. Kuma dukkanin kwamishinoni ku zasu baiwa takardar ajiye aikinsu a ranar Talata.

%d bloggers like this: