Bincike Labarai Sabon Labari

‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Rundunar ‘Yan Sandan ta bayyana cewa ta gayyaci Shugaban Jam’iyyar PDP da wasu jiga-jigan jam’iyyar na jihar Kano bisa kai wani farmaki da ake zargin wasu gurbattun matasan kwankwasiyya da kaiwa akan Ministan Sadarwa na Najeriya, Dr Ali Isa Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ranar Talatar data gabata.

A ta bakin mai magana da yawun Hukumar ‘Yan Sanda ta jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa yace sun gayyaci shugabancin jam’iyyar babban ofishin su a cigaba da binciken abin da ya auku domin kamu da gurfanar da duk wani mai hannu a ciki, kuma babu wani wanda hukumar zata bari muddin aka same shi da laifi.

Da yake hira da manema labarai a ofishin sa yace “Tabbas mun gayyaci Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, Darekta Janar na kamfe a zabukan 2019, Dr Yunusa Adamu ‘Dangwani, ‘Dan takarar Mataimkin Gwamna Kwamared Aminu Abdusalam, duk mun gayyace su ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ahmed Iliyasu dana darektan bincike n farin kaya.”

Ya kara da cewa “zuwa yanzu babu wanda ya shiga hannu amma ana cigaba da bincike domin ganin an gurfanar da wanda suka kaiwa ministan hari.”

A bangaren Jam’iyyar PDP kuwa da suke tabbatar da gayyatar da Rundunar ‘Yan Sanda tayi musu, ta bakin makogaron ta Malam Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya dora alhakin abinda ya faru kan masu tsaron lafiyar Ministan, inda yace babu ‘kwarewa a cikin aikin su.

Ya kara da cewa, a maimakon masu tsaron Ministan su bi ta hanyar manyan baki da filin jirgin saman ya samar, sai suka yi amfani da karfi wajen shiga ta cikin taron ‘yan kwankwsiyyar da sauran matafiya.

Inda yace, Shugaban Dari’kar tasu, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso saida yaja kunnen mabiyan sa kan bin dokokin hukumar filin jirgin saman tun da fari. Yace zasu amsa gayyatar Rundunar ‘Yan Sandan sakamakon burin su na son zaman lafiya da ci gaban tsaro a jihar dama kasa baki daya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Mutane sun fara suma, kafin zuwan Kwankwaso da Atiku filin Sani Abacha

Dabo Online

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Dabo Online

Wana laifi Dr Pantami yayi wa ‘Yan Kwankwasiyya da zasuyi masa ihun ‘Bamayi’ ?

Dabo Online

Ina tsoron karawa da Kwankwaso – Shekarau

Dabo Online

Zamu karbi sakamakon zabe, fatanmu a zauna lafiya – Kwankwaso

Dabo Online

KANO: Wata mata tayi yunkurin sace jariri

Dabo Online
UA-131299779-2