Copyrighted.com Registered & Protected

Atiku zai fuskanci matsin lamba inya dawo Najeriya – Lai Muhammad

Lai Muhammad, ministan yada labarai na kasa ya bayyanawa manewa labarai cewa tsohon mataimaki kuma dan takarar jam’iyyar PDP matakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar zai fuskanci matsin lambar daga hukumomin gwamnati saboda zai sha tambayoyi idan ya dawo Najeriya.

Ministan ya kara da cewa, zuwan sa kasar Amurka bai firgita gwamnatin don zamu kalubale da cin zabenta ba, sai dai ya tunasar da mutane cewa lallai gwamnati bataso ziyarar ba domin har shawara suka aika wa kasar Amurka dan kada su barshi ya koma shiga kasar.

Wai don ya tafi kasar Amurka, wannan hukuncin kasar ne amma Atiku ya sani cewa da zarar ya dawo kasar nan zai fuskanci hukumomin domin amsaa tambayoyi game da wasu makudan miliyoyin nairori daga tsohon Bankin Habib.

Ranar 13 ga watan Janairun shekarar 2009, Atiku ya karbi makudan kudi daga bankin na Habin, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar bankin.

%d bloggers like this: