//

Kasar Saudiyya za ta gayyaci Jay Z da Beckham don bude gidan rawa

Karatun minti 1

Gayyatar ya biyo bayan shirye-shiryen yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman Al Saud na maida kasar Saudiyya babban wajen shakatawa na duniya.

Jay Z, fitaccen mawakin Hip-Hop  dan asalin  kasar Amurka tare da tsohon dan wasan kwallon kafa, David Beckham zasu kasance manyan baki na musamman domin jagorantar kaddamar da wasanni.

Taron ya kunshi bada lasisin saka kida da abubuwan nishadi a gidajen cin abinci da kewaye, bude gidajen rawa da sauran abebadai da yariman ya kira da kayan more rayuwa.

Yarima yace sunayin hakan ne saboda kasar Saudiyya kasa ce ta matasa wadanda shekarunsu basu wuce 30 ba, don haka dole ne su basu rayuwa mai kyau ta yacce zasuji ba’a takura musu ba.

An samu sauye-sauye da dama a kasar ta Saudiyya, lamarin yana jan hankulan kasashen musulmai a kan yacce Saudiyya take sauya al’amuranta, wadanda suka sabawa koyarwar addinin Islama. 

A watan Fabarairun shekarar 2018, kasar ta ware dala biliyan 64 domin bunkasa harkar nishadi a kasar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog