Home LabaraiHawaye sun zubo daga Idon Sarki Sunusi yayin nuna alhinin mutuwar Jariri akan N1500

Hawaye sun zubo daga Idon Sarki Sunusi yayin nuna alhinin mutuwar Jariri akan N1500

by Dabo Online
0 comments

A wani faifan bidiyo, mallakar gidan Talabijin na Channels TV, an hangi mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, yana zubar da hawaye.

Hakan na zuwa ne bayan da yake bayarda labarin wata Mata da Jaririnta ya mutu akan kudi kasa da dalar Amurka 5, kwatankwacin kasa da Naira 1,560.

Sarki Sunusi a yayin da yake jawabi a gaban Kwamitin Cimma Muradun Karni da Majalissar Dinkin Duniya ta kafa, ya bayyana yacce tsananin Talauci yake addabawar mutanen Najeriya.

Sarkin ya kara da yin nunin cewa; Bambancin dake tsakanin Talakawa da masu Kudi a Najeriya, tazara ce mai nisan gaske.

“A lokacin da matar take jiran layi yazo kanta domin neman taimako, Jaririn nata ya mutu a hannunta.”

Sarkin ya bayyana cewa; Matar tazo neman taimakon kudi da bai kai dalar Amurka 5 ba domin samun kula da lafiyar Jaririn.

“Wannan shine abinda kullin yake faruwa a Najeriya.”

“Yara suna mutuwa saboda Iyayensu basu mallaki koda dala 5 ba, ace Uwa ta kalli mutuwar ‘danta akan kudi kasa da dala biyar.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00