Kungiyar Dalibai ta Kasa, wato NANS a takaice, reshen shiyya ta Uku, ta karrama Shugaban Sashin koyar da aikin Jarida ta Makarantar Nuhu Bamalli dake Zariya Malam Rabi’u Kera, da lambar yabo domin jinjina mashi bisa aiki tukuru da yake ba dare ba rana, domin cigaban shashin da kuma makarantar baki daya.
Da yake jawabi a wurin karramawar, Daraktan kula da harkokin Makarantu da tsare-tsare na Kungiyar, Kwamared Austin Amadi, ya ce, cikin tsare-tsaren ta, Kungiyar ta NANS, ta na lalubo wasu fitattu a cikin al’umma da suka yi fice ko nuna hazaka a rayuwar su, domin karrama su da kuma nuna su a idon duniya.
Kuma tun ba yau ba, sun jima suna samun labarin Malama Rabiu Kera, da irin jajircewar sa, wanda Kuma saboda jajircewar sa ne, suka kudiri aniyar karrama shi da lambar yabon da ake baiwa wasu zababbun mutane musamman a Makarantarantun gaba da sakandare.
Ya kara bada misali da wasu daga cikin ayyukan da ya gudanar lokacin sa ya fara jagorantar sashin a shekarun baya.
Ya kuma kwatanta shi, a matsayin mutum maras nuna ban-banci a fagen aiki, da yakan jawo kowwa kusa, domin daura shi matakin da ya dace saboda tafiyar da rayuwa bisa tsari.
Ya yaba masa saboda yanda ya daga darajar sashin koyar da aikin Jarida ta makarantar Nuhu Bamallin, ta zama daya daga cikin wacce ake alfahari da su a kasa baki daya, da ma irin ta ta jima tana yayewa da yanzu haka suka yi fice a duniya baki daya.
Da yake maida jawabi, Wanda aka karramar, kuma Shugaban sashin koyar da aikin Jarida ta Makarantar Nuhu Bamallin Malam Rabi’u kera, ya ce, duk nasarorin da aka samu, bai samu ba, sai da gudunmuwar daukacin ma’aikatan da suke aiki a tare da shi.
A saboda haka ne ma, ya sadaukar da lambar yabon kacokan ga daukacin ma’aikatan sashin.
“A yau sashin nan, ta yaye dalibai sama da Dubu Goma, Wanda kumayanzu haka sun zama gagara badau a wuraren da suke ayyukan su, kuma yanzu haka akwai kwasa-kwasai kusan guda hudu da ake aiwatarwa karkashin sashin”. Inji Rabiu kera.
Da ya juya ga karramawar da aka yi masa kuwa, ya godewa, Kungiyar ta NANS ne saboda zabo shi a cikin dubbai kuma suka karrama shi, sannan ya tabbatar masu da cewa, hakan zai kara mai azama ne da karsashi a aikin sa.
Shi ma a nashi jawabin, Shugaban dalibai da suke karatu a sashin koyar da aikin Jarida na makarantar ta Nuhu Bamalli Kwamared Bashir Abdullahi, Ya godewa karamcin da Kungiyar ta NANS ta yi masu ne, domin a cewar sa, karamci ne na Malam Kera da Sashin da kuma makarantar baki daya.
Kwamared Abdullahi, Ya kara tabbatar wa Shugaban sashin da sauran malaman da suke koyarwa, da samun cikakken hadin kai da goyon baya daga uwar Kungiyar ta su ta Kasa.
