Labarai

Sadiya Umar Faruq ta karyata rubutun da wani shafin Twitter yayi akan batun babu aurenta da Buhari

Minista Sadiya Umar Faruq, ta nesanta kanta da wani rubutu da wani shafin Twitter ya fitar mai dauke da sunanta inda inda ya bayyana cewa “Babu maganar aurenta da shugaba Buhari.

Tin dai da safiyar yau ne shafin ya fitar da wani rubutu a matsayin Ministar inda aka bayyana cewa; “Nida da shugaba Buhari da Aisha Buhari, mun dade muna alakarmu mai kyau. Babu maganar aure tsakaninmu.”

“Labaran da ake ta yadawa, ba gaskiya bane.”

Ministar ta shafinta na ainahi @Sadiya_Farouq, ta karyata rubutun da wancen shafin ya rubuta, ta kuma nesanta kanta da mallakar shafin.

Ministar dai tayi kira da mutane yada zancen shafin domin ba mallakinta bane kuma bata da alakar kusa ko ta nesa da shafin da mamallankanshu.