1
Gwamnati Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta, ta dakatar da Jami’anta daga tafiya kasashen Waje.
Sanarwar da mai dauke da sa hannun babban daraktan labarai na ofishin sakataren gwamati, Wille Bassey, tace ta dakatar da dukkanin mukarraban gwamnati da shugawabannin hukumomin kasar daga tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Wadanda suka shiga cikin dakatarwar sun hada da Ministoci da masu rike da manyan ma’aikatun kasar.
Gwamnatin tace tayi haka ne domin baiwa ‘yan Majalissu damar yin aiki zartar da sabon kasafin kudin shekarar 2020.
