Bidiyon maganar yana chan kasa.
Biyo bayan yunkuri da fafutukar karfafar harkokin Nishadi da yariman kasar Saudiyya, Muhammad Bn Salman, yake yi, Malamai a kasar sun fara nemo wa shirin yi wake-wake da kayan sauti zamani hujja a cikin Musulunci.
Daga cikin malamin dai yace; “Tin lokacin Manzon tsira, Annabi Muhammad SAW, ana yin waka tare da yin kida da kayan sauti na wancen lokacin.”
DABO FM ta rawaito daga cikin malaman, Sheikh Adil al-Kalbani, limamin wani masallaci a birnin Riyadh, ya kawo wani Hadisin ya yace; Uwar Muminai, Aisha Bn Abu Abkr (Allah ya kara yarda a gareta) tayi waka tare da wasu makotanta guda biyu.
Malamin ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da yayi da gidan Talabijin na SBC dake kasar ta Saudiyya.
Sheikh al-Kalbani, ya sake fadar wani hadisin da yace; Manzon Allah SAW, ya ga wata mata, ya tambayi Uwar Muminai, Aisha R.A, ko ta san matar?. Bayan da ta amsa cewa bata santa ba, sai Manzon Allah SAW yace; Wannan itace Qena, mawakiyar zamaninmu” har ma kuma ya tambayeta ko zata yi mata (Aisha RA) waka.
Shehin Malamin ya kara bayyana cewa; Manzon Allah SAW; ya halarci taron daurin aure inda matar (Qaina) ta rera waka tare da ganga.
Ya yi nuni da cewa Hadisan sun hada tarihin al’ada tare da samun asali a bangaren Musulunci.
Sai dai jamhurin Malaman kasar da ake wa lakabi da ‘Orthodox Muslim’, sun cigaba da bayyana haramcin kade-kade.
