Labarai

An saukar min da wahayi zanyi shugabancin Najeriya -Yariman Bakura

Tsohon gomnan Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura yace zai tsaya takarar shugaban kasa saboda wahayin da aka saukar masa ta hannun abokin sa.

A rahoton da Dabo FM ta samu ta gidan talabijin na SVTV News, Yariman bakura ya bayyana cewa “Ni kafin nace ‘kala, mutane sunce ‘kalu.”

“Akwai wani abokina na da mukayi sakandare tare wanda lokacin da muka zo muna jayayya da Mahmuda shi yana kwamishinan sa amma dai bamu bata ba muna gaisawa muna mu’amala shine ya bugo min waya yake gaya min”

“Yake gaya min yaje Makka umara tare da matar shi da danshi, wani balarabe ya tsaida shi a kofar harami yayi masa sallama, yace mishi..”

“Ku yan zamfara ko?”

“Ba cewa yayi ku daga zamfara kuke ba, sai abokin nawa yace: Na’am”

Balarabe yace “ina babanmu sanata Ahmed Sani Yariman Bakura?”

Sai yace mishi “yana nan lahiya kalau ai ni abokina ne kuma dan uwana ne”

Sai yace “to in kunje ku gaya mishi zaiyi mulkin Najeriya indai ba ya mutu ba kuma kuce ina gaishe shi”

Suna juya wa saiya bace

Karin Labarai

Masu Alaka

Shawarata ga Shugaba Buhari kan yadda za’a magance tsaron Borno da Zamfara, Daga Datti Assalafiy

Dabo Online

Najeriya Muna Da Gajen Hakuri Wallahi,shin ko za mu tuna

Rilwanu A. Shehu

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin ta sake jaddada kudurinta na fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Dabo Online

2023: PDP ta shiga neman sabon dan takarar shugabancin kasa da zata tisa a gaba

Muhammad Isma’il Makama

Tsintsiyar Najeriya ta kafa tarihi, tafi kowacce girma a duniya

Dabo Online
UA-131299779-2