Home LabaraiEFCC tayi nasarar chafke Ibrahim Magu na karya a Fatakwal

EFCC tayi nasarar chafke Ibrahim Magu na karya a Fatakwal

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Hukumar yaki da cin hanici da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya EFCC ta ce ta cafke wani mutum da yake sojan-gona a matsayin shugaban hukumar wato Ibrahim Magu.

Rahiton Dabo FM da BBC ta ta rawaito cewa Ofishin hukumar na garin Fatakwal ne ya cafke “Ibrahim Magu” a ranar Laraba, kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.

“Yana amfani da sunan ne wajen zambatar jama’a tare da bata sunan wasu manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Delta ta NNDC,” in ji EFCC.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00