1
Yan bindiga sunyi garkuwa da Hakimin Birnin Gwari, Yusuf Abubakar a kan titin Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba.
Daily Nigerian ta rawaito cewa an sace hakimin tare da wasu daga cikin masu rike da sarautar yankin wadanda suka hada da Sarkin Kudun Birnin Gwari da wakilin Makarantar Birnin Gwari, Ibrahim Musa.
Ta tabbatar da dauke a wajejen karfe 12 na rana a Unguwar Yako.
