//
Friday, April 3

Bayan rahotan Dabo FM, wata gidauniya za ta kai dauki zuwa Makarantar Firamare ta garin Garo

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wata gidauniyar jinkai mai sunan, Hadeeyatul Khair Foundation, da wasu matasan mata a jihar Kano ke jagoranta, sun shirya baiwa makarantar Firamaren dukkanin abinda take bukata.

Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da DABO FM tafitar a ranar 5 ga watan Disamba, wanda ya nuna irin halin ko in kula da makarantar take ciki na rashin dukkanin wasu muhimman kayayyakin karatu.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun shugabarta, Mufida Fari, ta bayyana shirinsu na ziyartar makarantar domin kai taimako.

“Suna bukatar kusan dukkanin kayyakin karatu da suka hada da ginin ajujuwa, kujeru, tebura, litattafai da kayyakin rubutu.”

Shugabar ta bayyana zasu fara kaiwa makarantar Litattafai da kayayyakin rubutu a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba, sa’an ta shiga shirin tattaro kudade don gyaran makarantar baki daya.

Masu Alaƙa  Attajirar Najeriya ta bawa Najeriya tallafin Naira biliyan 1, zata rabawa Zaurawa da Marayu N25,000

“A wannan makon, 22/12/19, zamu fara kai ziyarar makarantar domin rarraba musu litattafai da kayayyakin rubutu.”

Shugbar ta kara shaida bin wasu daga cikin Gidauniyar jinkan al’umma domin samu isassun kudaden aiwatar da ayyukan da makarantar take bukata.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020