Home LabaraiKu nemi shawara a wajen mutanen kirki – Shawarar Buhari ga manema Aure

Ku nemi shawara a wajen mutanen kirki – Shawarar Buhari ga manema Aure

by Dabo Online
0 comments
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban Muhammad Buhari, yayi kira da masu ma’aurata musamman wadanda sukayi aure a wannan lokacin dasu rika neman shawara a wajen mutanen kirki duk lokacin da wani abu ya shige musu duhu.

Sashin Hausa na Legit.ng ya tattaro cewa shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Disambar 2019 a wajen taron daurin auren dan gidan shugaban Majalissar Dattijai, Sanata Ahmad Lawam.

Idan kuna neman wasu shawarwari kan rayuwa, wanda ya shafi kowani bangare, ya zama dole ku mayar da hankali sannan ku koya aga mutanen da ke da shaida mai kyau.

“Mutum nagari abun koyi shine Sanata Lawan. A siyasa da rayuwa, ya tara kyawawan dabi’u,”

Shugaban kasar ya bayyana a wani sako da wata tawaga wacce ta hada da ministan Abuja, Mohammed Musa Bello, na tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (rtd), na noma, Sabo Nanono da kuma na sufurin jirgin sama, Hadi Sirika suka gabatar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00