Home LabaraiKansiloli 11 cikin 13 sun amince da tsige shugaban karamar hukumar Zariya

Kansiloli 11 cikin 13 sun amince da tsige shugaban karamar hukumar Zariya

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

Kokarin tsige shugaban karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim, ya gamu da cikas saboda kasa isar rubutacciyar takardar dakatarwar ga sakataren mulki ta karamar hukumar, wanda dama a doka shi ke da alhakin amsa.

Da yake tabbatar da hakan ga Dabo FM a Zariya, shugaban masu rinjaye na majalisar kuma Kansila mai wakiltar gundumar Kufaina, Hon Akilu Abubakar, ya ce, takardar tsigewar na kumshe ne da wasu daga cikin dalilan daukar matakin.

“Kadan daga cikin dalilan su ne, rashin iya gudanarwa da rashin kammala ayyukan raya kasa da aka faro da kuma bada kwangilar bogi a wasu gundumomi kamar Dutsen Abba da Anguwar Fatika da Sakatariyar karamar hukuma da dai sauran su.

A cewar shi, a baya sun naimi shugaban majalisar, ya zo gaban su ya gurfana domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suke masa da kuma zargin yin kurman kasafi a shekarar 2020, amma ya yi biris da umarnin nasu.

“A shekarar 2019 da ta gabata, babu wani babban aiki na raya kasa da aka aiwatar a fadin karamar hukumar.” A cewar Hon Akilu Abubakar.

Bisa wannan ne, majalisar ta aminta da kafa wani kwamiti da zai zagaya dukkanin wuraren da aka gudanar da ayyukan domin tabbatar da ingancin su.

Sai dai a cewar shugaban kwamitin, Hon Yusha’u Muhammad, abun da suka gani a zagayen da suka yi, ya tayar masu da hankali matuka, saboda kasa cika al-kawurran da shugaban karamar hukumar Zariya ya yi a lokacin yakin neman zaben su.

“Bisa wannan ne, ‘yan majalisar 11 cikin 13 suka sanya hannu tare da amincewa su tsige shugaban karamar hukumar.

Sai dai tsigewar taci karo da wasu abubuwa da suka faru lokacin da suka je sakatariyar karamar hukumar domin mika takardar ga sakataren mulki na karamar hukumar, Alh Abdullahi Sani, domin kuwa sun samu baya nan a ofishinshi duk da cewa ranar aiki ce.

Kansila mai wakiltar mazabar Anguwan Fatika, Hon Yusha’u Muhammad, ya kara da cewa, sashi na 9, 1,2,3 da kuma 4 cikin baka na kudin tsarin gudanarwa, ya basu dama karara na tsige shugaban karamar hukuma idan an same shi da wasu laifuka.

Sai dai matakan tsigewar sun hada da a gabatar da rubutacciyar takarda ga sakataren karamar hukumar, shi kuma cikin kwanaki 7 ya gabatarwa Babban mai Shari’a na Jiha. Daga nan shi kuma ya duba tare da kafa kwamiti da za su zauna akan wannan takardar daga bisani kuma kotu ke da ikon tabbatar da tsigewar.

Sai dai da yake nashi tsokacin, Kansila mai wakiltar mazabar Tukur-Tukur, Hon Isra’ila Shu’aibu, ya ce, babu gudu babu ja da baya akan matsayin nasu, kuma za su ci gaba da bin matakan da suka dace domin ganin hakar su ta cimma ruwa.

Da Dabo FM ta tuntubi sakataren karamar hukumar Alh Abdullahi Sani, wanda shi ke da hakkin karbar takardar tsigewar, ya tabbatar mana cewa bai karbi takardar ba. Kuma yace bashi da ikon yin magana akan wannan batu, sai dai a tuntubi mai baiwa shugaban karamar hukumar shawara akan harkokin siyasa shi ke da alhakin magana da mu.

Dama tuni dangantaka ta yi tsami tsakanin bangaren zartaswa da na dokokin karamar hukumar ta Zariya. Kuma ko kwanakin baya, Kansilolin sun yi yunkurin dakatar da shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim, amma hakan bai yiwu ba saboda shiga tsakani da magabata suka yi.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00