//
Friday, April 3

Bayan biliyan 1 na gyaran makabartu, Matawalle zai gina sabon gidan gwamnati na biliyan 7

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kwanaki kadan bayan ma’aikatar addinai ta mika kasafin kudinta na Naira Biliyan1 domin gyaran Masallatai da makabartu, gwamnatin ta fara shirin ginin sabon gidan gwamnatin jihar akan kudin Naira biliyan 7.

Sakataren gwamnatin jihar, Bala Bello ne ya bayyana haka yayin da yake kare kasafin kudin da ofishinshi yayi a cikin kasafin kudin jihar na shekarar 2020.

DABO FM ta tattaro Bala, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 2 ga Janairun 2020 a gaban zauren Majalissar dokokin jihar dake garin Gusau.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zata gina sabon gidan gwamnatin ne kasancewar akwai bukatar a samar dashi.

”Gidan gwamnatin da ake amfani dashi yanzu, tsohuwar Sakatariyar karamar hukumar Gusau ce tin lokacin da ake hade da jihar Sokoto.”

Masu Alaƙa  ‘Yan Bindiga da dama a Zamfara sun zubar da makamansu tare da neman yafiya - Matawalle

“Muna bukatar sabon gidan gwamnati domin mu shiga sahun jihohin da suke da na zamani.”

“Haka zalika munyi la’akarin da karancin ofisoshin gwamnati wajen ginin sabon gidan gwamnatin.”

Bello ya bayyana cewa idan aka kammala sabon gidan gwamnatin, za’a mayar da tsohon gidan ya zama babbar Sakatariyar jihar.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020