Rahotanni daga garin Agadez, sun bayya yacce aka samu saukar dusar Kankara mai yawa a garin dake arewacin Jamhuriyar Nijar.
A wani rahoto da gidan rediyon Freedom dake jihar Kano ya fitar, ya tabbatar da saukar dusar Kankara a garin.
DABO FM ta tattaro cewa; Mazauna garin sun cika da mamakin kasancewa basu taba gani dusar Kankara ta sauka mai yawan gaske a garin ko kuma garuruwan da suke makwaftaka ba.
“Garin Agadez dai kusan shine gari mafi zafi a Jamhuriyyar ta Nijar, amman kuma gashi sabo tsananin sanyin bana harda dusar kankara”
Harsashen masana na birnin Agadez ya nuna akwai tsananin sanyi da disar ruwa-ruwa bisa ma’aunin ‘Celcious’ 7.
Haka zalika hasashen ya nuna akwai guguwar bazata mai karfin gudun kilomita 69 cikin sa’a 1. Hasashen ya kara nuna akwai iska da take kadawa gabas mai karfin kilomita 46 a sa’a 1.
