Kungiyar Kwadago reshen jihar Niger, ta baiwa gwamnatin jihar Niger wa’adin kwanaki akan fara biyan sabon albashin N30,000 ko kuma ta tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.
Kungiyar ta bayyana haka ne a yayin wani taron gaggawa da ta gudanar ranar Juma’a a garin Minna.
DABO FM ta tattaro cewa kungiyar ta ce ba ta da wani zabi da ya wuce ta bayar da wa’adin tare da fadawa cikin yajin aikin idan gwamnatin jihar bata amsa ba.
A wata takardar da mai dauke da sa hannun shugaban Kungiyar, Kwamared Yakubu Garba da shugaban ‘yan kasuwar jihar, Kwamared Yunusa D. Tanimu, sun yi kira da gwamnatin da su kaddamar da fara biyan sabon albashin da sauran basussuka kafin ranar Litinin, 4 ga watan Fabarairun 2020.
Daily Trust ta tattaro cewa cikin kasafin kudin jihar na shekarar 2020, gwamanti ta sanya albashin ma’aikatan jihar a N30,000 a matsayin mafi karanci. Sai dai har yanzu ba’a san yaushe gwamantin zata kaddamar da fara biyan sabon albashin ba.
