Gwamnatin jihar Kwara ta amincewa da maida wa alhazan jihar da suka je hajjin shekarar da ta shude canjin da aka samu na Naira miliyan 21.
Sakataren hukumar Alhazan jihar, Alhaji Muhammad Tunde-Jimoh ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta gabata, kamar yacce kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito.
Ya bayyana cewa wadanda suka biya kudadensu kuma wani abu yasa basu samu damar zuwa ba da wadanda suka rasu, to lallai za’a maida musu da kudadensu.
Sakataren dai yace hukumomin kasar Saudiya ne suka maido da kudaden a matsayin ragowar kudaden da mahajjatan basu kashe ba a lokacin zamansu a kasa mai tsarki.
Tini dai hukumar tace a yau Laraba, mahajjatan karamar hukumar Ilori ta yamma suje babbar hedikwatar hukumar inda kuma ranar Alhamis, ta bukaci mahajjatan kananan hukumomin Asa da Ilorin ta kudu suje ofishin hukumar.
Ranar Juma’a kuwa, mahajjatan Arewacin Ilori da karamar hukumar Moro ne zasu je inda mahajjatan Sanatoriya ta Kudu zasu je ranar Litinin.
Haka zalika hukumar ta bukaci mahajjatan da su je ofishin tare da Fasfo da takardar shaidar biyan kudin Hajjin 2019.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN yace jihar Kwara tana da adadin 2,026 wadanda suka tafi tare da hukumar alhazan.
