‘Yar Najeriya, Musulma ta lashe kambun gwarzuwar nahiyar Afirika karo na 4

https://twitter.com/CAF_Online/status/1214642368231727104

Kyaftin din Super Falconets ta Najeriya da kuma yar wasan gaba ta kungiyar kwallon kafar Mata ta Barcelona, Asisat Oshiola, ta lashe kambun gwarzuwar yar wasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika.

Wannan ne dai karo na 4 da ‘yar wasan, Asisat Oshiola ‘yar jihar Legas take lashe kambun, inda ta lashe a shekarar 2014, 2016, 2017 da kuma shekarar 2019.

Yar wasan da take taka leda a kungiyar Barcelona ta kasar Spaniya, ta taka leda a kungiyar Dalian FC dake birnin Nanjing na kasar Sin, kafin nan kuma ta taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake birnin Landan na kasar Birtaniya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.