Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin fara biyan ma’aikatan jihar da sabon albashin N30,000 na mafi karanci.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar 10 ga watan Janairu bayan kammala karbar sakamakon zaman dai-daiton kwamitin da aka kafa domin tattaunawa tsarin biyan albashin.
Kamfanin dillancin Najeriya, ‘NAN’ ta rawaito cewar gwamnan yace ma’aikatan jihar zasu baya karbar albashinsu na N30,000 daga watan Janairu.
Gwamna Tambuwal ya alkauranta biyan dukkanin basussukan da karin da ma’aikatan suke bi inda ya bayyana an samu rike kudaden ne bisa yunkurin gwmnati na kakkabe baragurbi a cikin ma’aitakan.
Ya kuma gode wa kwamitin tattauana tsarin biyan albashin bisa aikin da sukayi wanda a kawo karshe a zaman da aka gudanar yau Juma’a.
