Home LabaraiDan Majalissar wakilai daya tilo da ya kai kudiri 34 bayan rantsar da majalissa ta 9

Dan Majalissar wakilai daya tilo da ya kai kudiri 34 bayan rantsar da majalissa ta 9

by Dabo Online
0 comments

Bayan wani bincike da ya bayyana cewar mafi ya yawan ‘yan majalissun wakilan suna zaman kashe wando ne a zauren Majalissa, DABO FM ta binciko dan Majalissar da ya kai kudiri 34 tin bayan rantsar da sabuwar Majalissar.

Dan Majalissa Muhammad Tahir Monguno, bulaliyar Majalissar, dan majalissa wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Monguno,Marte da Nganzai dake jihar Borno a arewacin Najeriya.

DABO FM ta tabbatar da cewar Muhammad Tahir Monguno shine dan majalissa daya kacal da ya kai kudiri 34 tin bayan rantsar da Majalissar Najeriya ta 9, kamar yacce shafin Majalissar na yanar gizo-gizo ya nuna.

Kuduran da dan majalissar ya shigar sun hada da; Kudurin samar da Cigibiyar Kula da Idanu ta kasa a jihar Kaduna, Kudurin samar da makarantar karatun gwaje-gwajen jini, kudurin samar da hukumar kula da ‘yan gudun hijira, bakin haure da masu bukata ta musamman, kudurin kara samar da makarantar horas da ‘yan Sanda.

Ga dai jerin cikakkun kudure-kuduren da dan majallisar ya shigar; (Daga shafin Majalissar ta kasa)

Muhammad Tahir Mungonu

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00