A yau Laraba, 15 ga watan Janairun, 2020, mai girma, Sir Ahmadu Bello, Sardauna ya cika shekaru 56 bayan da Manjo Nzeogwu ya kashe shi.
DABO FM tayi waiwaye a yanayi na tunawa da wannan rana mai cike da bakin ciki ga dukkanin al’ummar da suka san darajar dan adam.
A yayin wata tattaunawa da tsohon babban sakataren Marigayi Sardauna, Gidado Idris yayiwa da sashin Weekly Trust na jaridar Daily Trust a shekrar 2015.
Gidado, ya bayar da tarihin yacce Manjo Nzeogwu ya kashe Sardauna har lahira a ranar 15 ga watan Janairun 1966. Gidado Ibrahim ya kasance babban sakatare na hannun daman marigayi Sir Ahmadu Bello a wancan lokacin kuma tsohon sakataren gwamnatin Najeriya a zamanin Janar Sani Abacha.
Ya fara da; “Da yammacin kafin faruwar bala’in , a ranar 14 ga watan Janairun shekarar 1966 da misalin karfe 8 na dare, tsohon Firaminista marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, ya kira don yin magana da Sardauna. A lokacin babu abinda yake yi, sai na hada su sukayi magana.
Bayan wannan lokacin, Sardauna ya kirani yana son sanin yawan basussukan da ake binshi na abubuwan da muke karba a shagunan Kingsway, Bhojson da Et Cetera.
“Wajejen karfe 12, ya kirani tare da akawunshi, Aliyu Kangiwa, wanda yace muje mu ga sabon ofishinshi wanda mu 3 muka dunguma muka tafi. Yayi farinciki da sabon ofishin nashi. Tin kafin nan, an sanar masa cewar shugaban yankin kudancin Najeriya, Sameul Akintola, zai zo ganinshi amma lokacin yana da tsawo kafin zuwanshi. Sai ya yanke bazai je taro shi a filin tashi da saukar jirage ba, sai ya tafi masallacin domin yin sallar Juma’a bayan ya tura minista S.L Akintola ya taro shi.
“Duk wannan lokacin azumin Ramadan ne.”
“Wauraren karfe 3 na rana akace mana shugaban yankin yammacin Najeriya ya sauka har ma yana kan hanyarshi ta zuwa gidan Janar Usman Hassan Katsina dake kawo, wanda shine a ya zai ya zama sabon gida da ofishin Sardauna. Na tuna lokacin a tare dashi akwai Remi Fani Kayode da sauran minsitoci.
“Shugaban yammancin Najeriya, Akintola yace yazo ne don ji daga wajen Sardauna cewar ko yana da masaniyar cewa Sojojin suna da shirin karbe gwamnati daga hannayensu. Sardauna yace masa eh lallai yasan da abin amma ya bar komai a hannun Allah.
“Akintola yace wa Sardauna yazo da jirgi, wanda zasu iya tserewa zuwa kasashen ketare kamarsu Nijar, inda aminishi take shugabancin kasa a wannan lokacin. Sardauna yaki amincewa da haka sa’annan yace ai wadanda suke son kwace gwamnatin, tin da fari basu suka bayar da mulkin ba. Sardauna yace masa; ‘Bazan bar mutane na in tafin wani waje don in zauna ba a lokacin da suke bukata ta. Haka zalika ya baiwa shugaba Akintola shawarar cewar; tin da yasan abinda zai faru, ya koma yankinshi ya sanarwa da mutanenshi don sun shirya abinda yakamata suyi. Daga nan shugaba Akintola ya dauki shawarar Sardauna, ya kuma koma garin Ibadan.”
DABO FM ta tattara cewar Gidado Idris ya bayyana cewar bayan shugaba Akintola ya tafi, lokaci ya kurewa Sardauna wanda har bai samu yaje yin wasan da yafi so ba. Inda a nan ne ya yanke shawarar yin shawagi a cikin gari da kuma kudancin Kaduna kafin lokacin yin buda baki. -Duk lokacin a watan Ramadana ne.
“Mun dunguma cikin wata mota da take da tsayi, mai kujeru dake kallon juna. Babban direban Sardauna, Ali Kwarbai wanda ake ce masa Sarkin Mota ne yake tukamu a wannan lokacin. Yana tare da abokanshi suna kallon juna. Babu abinda muke cewa lokacin da ake tafiyar har zuwa lokacin da aka gama shawagi, muka dawo gida duk kafin lokacin buda baki.
“Yana da kyau a gane cewar a wancen lokacin shugabancin, aiki ne na kullin kuma koda yaushe, babu hutun mako na Asabar ko Lahadi. Idan muka fita daga gida tin safe, yawanci muna dawowa ne tsakar dare, wannan shiyasa dayawa daga cikin ‘ya’yanmu basu sanmu ba. Muna barin gida tin 5 na safe domin bama so mu kara zuwa wajen Sardauna ko da da karin minti daya ne.
Ranar Bakin cikin
Gidado Ibrahim yace; “A wannan daren bayan shan ruwa, Dan Kwairo yana wajen Sardauna wajejen karfe 10:30 na dare. A lokacin duk mun gaji amma babu yadda muka iya. Ya cigaba da wakenshi har zywa wajen 11:30 na dare, lokacin da Sakataren gwamnatin Arewa, Alhaji Ali Akilu, Kwamishinan ‘yan sanda, M.D Yusuf da Birgediya Janar Samuel Ademulegun, dukkaninsu suka zo suna son ganin Sardauna. Bayan zuwansu, sun samu ganawa da Sardauna na tsawon mintuna 30 kafin su tafi.
“Har lokacin da suka fito, Dan Kwairo yana tayin wakarshi, anan ne yayi sallama ya hau sama domin ya rubuta sakon barka da sallah, ya kuma yi bacci a inda mu kuma da safiyar gobe zamu tafi Sokoto. Mun dade anan muna ta hira da dare yayi kuma mukaga Sardauna bai neme mu ba sai muka tafiya gida.
Har da muka futo bamu lura cewar tuni Sojoji sun zagaye gidan ba. Ina zaune a unguwar Doka Cresent a wancen lokacin, a lokacin da muka fita, naji karar jiniwa.
“Da naji karar wanan jiniyar sai ban kawo komai ba saboda muna gwada daga lokacin zuwa lokacin don muji ko bata lalace ba. Sai kuma ni da Haruna Musa (Sakataren tsare-tsare), mun hangi mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, wani mutumin kabilar Idoma da sunanshi ya kwanta min, ya nufi gidan Sardauna. Amma duk da haka ban kawo komai ba.
Abubakar Umar, Sakataren Sardauna na musamman, wanda ya yake a sashin baki na gidan, yaji hayaniya, wanda bayan leko ta windo, yaga Sojojin a ko ina. Daga nan ne ya dauki waya ya kirawo sakatare Ali Akilu, ya kuma sanar dashi abinda yake faruwa, yana tsammanin juyin mulki ne.
Bayan ya sanar da Akilu, cikin gaggawa ya shirya ya tafi gidan M.D Yusuf. Mintuna 5 bayan fitarshi, Sojojin suka gazaye gidanshi, suka tambayi matarshi yana iya, tace musu ya tafi Zaria wajen wani taro, sannan suka tafi. Wannan wayar da Abubakar Umar yayi masa, itace ta sa ya kubuta.
Ya bayyana cewa a lokacin, sojan da ya kashe Sardauna, Janar Chukwuma Kaduna Nzeogwu, ya fito da kowa na cikin gidan yace sun kwanta, wanda ya hada da matan Sardauna da dukkanin masu aikace-aikacen gidan.
“Janar Nzeogwu da kanshi ya tambayi cewar “Wanene Ahmadu Bello a cikinku?” a lokacin akwai dan gidan da suke kama da Sardauna, yace shine Ahmadu Bello, sai dai bai kai Sardauna a tsaye ba. Suka ce bashi bane. Daga nan ne suka ce idan ba’a fada ba, duk zasu harbesu.
“Sardauna a mike yace musu “Nine wanda kuke nema”, yayi nuna ga matanshi 3 su matsa daga gefenshi. Da Sojojin suka yunkuro kasheshi, biyu daga cikin matan sai suka tashi, ita uwargidan taki tashi tace idan za’a kasheshi, to itama a hada da ita. Suka kashe su tare su biyu a yanayin da sun rungume juna bayan ta kankameshi.
“Sun bar gawarwakin a inda muka sameshi.
“Gurin duk ba kowa. Ministoci duk sun tafi. Anan muka yanke shawarar cewar mu kaisu gidan Sultan dake unguwar Sarki, wanda bayan munyi haka ne muka shirya su, anan ne aka binneshi.
