A wani yunkuri na nuna goyon bayan adawa da rundunar Amotekun, kungiyar Miyetti Allah kautal hore ta yi wani kakkausan gargadi ga gwamnonin Kudu maso yammacin Najeriya bisa kaddamar da rundunar da za ta samar da tsaro a shiyyar.
Gargadin da ya samu sa hannun babban sakataren kungiyar na kasa, Alhassan Saleh, ya bayyana cewar wannan yunkuri tamkar barar da damar yankin ce ta futar da kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.
Sakataren kasar yace wannan abu ya basu mamaki matuka. Kuma ya jijjigasu. Domin kuwa a cewarsa idan har suka samu damar shugabancin kasa, wane hali yankin zai kasance musamman ga kabilar fulani?
Daga karshe ya nuna jin dadinsa ga kalaman da babban ministan shari’ah yayi na haramta gamayyar. Domin ya kamata ace tun dadewa kafin lamarin ya karfafa aka dakatar da shi. Don haka kamar yanda babban lauyan gwamnatin ya kalubalanci rundunar tsaron, su ma suna kan wannan mataki.
