//

An ceto Matar dan majalissar Jigawa da ‘yan binduga suka sace

0

Rahotanni daga iyalan Hajiya Zahra’u Aliyu, sun bayyana DABO FM dawowarta gida bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita.

DABO FM ta tattara cewar da asubahin ranar Asabar, 11 ga Janairu, ‘yan bindiga su 3, sukayi garkuwa da Hajiya Zahra’u Aliyu, kamar yadda kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, DSP Abdu Jingiri ya bayyana.

Hajiya Zahra’u ta koma gidanta a daren jiya Laraba da misalin karfe 11 na dare cikin koshin lafiya, kamar yacce majiyoyin ganin ido suka tabbatar mana.

Sai dai ko da muka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar domin jin ta yadda rundunar ta ceto Hajiya Zahra’u, wayarshi a kashe a har zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020