//
Friday, April 3

El-Rufa’i zai kaddamar da shirin bada ilimi kyauta a Kaduna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Dr Shehu Makarfi ya bayyana tini gwamnatin jihar ta shirya tsaf domin kaddamar da shirin bada ilimi kyauta tun daga matakin firamare har sakandare.

Dabo FM ta rawaito, Dokta Makarfi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan fitowa daga wata ganawa da shuwagabannin makarantun sakandare na jihar baki daya.

Ya kuma bayyana cewa satin daya gabata ma yayi tattanawa da masu ruwa da tsaki na ilimi a fadin jihar Kaduna. Kamar yadda DailyNigerian ta fitar.

Makarfi ya kara da cewa wannan shirin daban yake dana baya domin zai hada da kafatanin makarantun firamare, sakandare ta maza data mata, karama da babba, wanda shirin na baya ya hada ne da kananan makarantun sakandare na mata kawai.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020