Muhammad Sa’id Jammal dan Najeriya dake zaune a Abuja ya ginawa matarsa gida mai kirar jirgin sama saboda soyayyar ta da son tafiye tafiye, iyayen Jammal yan asalin Labanon ne amma yana dauke da shaidar zama cikakken dan Najeriya.
Rahoton Dabo FM ya bayyana cikin wata hira da BBC Pidgin, yace a kowane lokaci ina so matata idan tana cikin gida ta dinga jin kamar tana sararin samaniya cikin jirgi ne, saboda yanda take son tafiye tafiye.

Ya kara da cewa “Na fara gina gidan ne tun 1999 amma har yanzu ina kan karasawa, duk da dai muna cikin gidan.”

Jammal ya kara da cewa “Mutane na tambaya ta meyasa ban gida wannan gida a kasa ta ba, ina basu amsa da ni bani da wata kasa da ta wuce Najeriya, mahaifina yazo najeriya kafin a bada mulkin kai a shekarar 1960.”
Jammal yana da ‘ya ‘ya 6 kuma duk an haifaffun Najeriya. Wannan gini dai yana daukar hankalin matafiya da dama.
