Labarai

Buhari ya bada umarnin kubutar da dan Najeriya dake jiran hukuncin kisa a Saudiyya

Bayan rahoton Dabo FM na sake maka wani dan Najeriya da ake zargi da fasa kwarin kwayoyi zuwa kasar Saudiyya, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bawa atoni janar na Najeriya, Abubakar Malami umarnin ayi duk mai yiwuwa domin kubutar da wani dan asalin jihar Zamfara dake jiran hukuncin rataya a kasar Saudiyya. Kamar yadda TheCable ta bayyana.

Umarnin ya biyo bayan wani tattaki da gwamnan jihar Zamfar, Bello Matawalle yayi domin an kubutar da Ibrahim Ibrahim daga hannun hukumomin Saudiyya wanda suka zartar masa da hukuncin kisa bayan sun kama shi da laifin shigo da kwayoyin ‘Tramadol’ da akayi mishi cushe a filin jirgin sama.

Kwanaki kadan da suka shige Dabo FM ta binciki lamarin inda tabbatar da cewar hukumomin kasar ta Saudiyan dai sun maka Ibrahim duk da hukunci Kotun Jidda tayi na wanke shi daga zargin shigar da wata jaka cikin kasar ai dauke da kwayar ‘Tramadol’

Idan ba’a manta a ranar 30 ga watan Afirilun 2019, hukumomin Saudiyya suka sake wasu ‘yan Najeriya ciki har da matashiya Zainab Aliyu bayan rashin samunsu da aikata laifin shiga cikin kasar da kwayar ‘Tramadol’ da kuma shigar gwamnatin Najeriya cikin lamarin.

Bisa ga takardun da muka tabbatar, an kama Ibrahim Ibrahim tin a daren ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2017, bisa umarnin hukumar hana fasa kauri da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, jami’an tsaron kasar ta Saudiyya sukayi awon gaba da Ibrahim zuwa ofishinsu domin gudanar da bincike. A inda ya bayyana musu cewar bashi da masaniyar jakar da kwayoyin suke ballantana ayi batun ya shigo dasu cikin kasar.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi suka cigaba da tsare Ibrahim domin gudanar da bincike akan zargin da akeyi masa. Hukumar ta fitar da takarda mai lamba 1703203, wanda tace ta samu kwayar ‘Tramadol’ kimanin 1497 a wata jaka mai dauke da sunan Ibrahim Ibrahim Abubakar.

Hakan yasa sun cigaba da tsare shi har zuwa ranar da aka aike dashi kotu domin fara gudanar da shari’a.

Karin Labarai

Masu Alaka

Zuwa ga Shugaba Buhari: Idan kai mai gaskiya ne, ka tonawa barayin kusa da kai asiri – Gwamnan Akwa Ibom

Dabo Online

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya kara wa’adin gwamnan babban bankin Najeriya ‘CBN’

Dabo Online

2023: Zuwa yanzu bani da niyyar ‘kara tsayawa takara a karo na uku -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Rikici tsakanin kabilun Tiv da Jukun yana damu na – Buhari

Dabo Online

Gobe Alhamis, Buhari zai tafi kasar Saudi Arabia

Dabo Online
UA-131299779-2