//
Friday, April 3

Rikicin Siyasa: Ganduje ya sake gina Masallacin da Kwankwaso ya rusa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin jihar Kano karkashi jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sake gina Farin Masallaci wanda tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso ya rushe zamanin yana gwamna.

Rahoton Dabo FM ya tabbatar da sake ginin masallacin dake kan titin Kano zuwa Zaria, Kwankwaso dai ya rushe masallacin ne bisa kokarin fadada titin na Zaria, tare da anyi masallacin a kan hanya ba tare da izinin gwamnati ba.

Tini Gwamna Ganduje yayi alkawarin gyarawa a wancan lokaci bayan da dambar war siyasa ta shiga tsakanin sa da tsohon gwamna Kwankwaso.

Wanda manazar tan siyasa ke ganin dowo masallacin ma siyasa ce ta jawo bisa laakari da yana kan hanyar dai, inda ake ganin da Ganduje ya bada wani filin gami da sake ginin Farin Masallacin wanda nan gaba idan wata gwamnatin tazo kara fadada titin bazai shafi masallacin ba.

Masu Alaƙa  Har yanzu Abba Kabir Yusuf muka sani a matsayin dan takarar gwamnan PDP - INEC

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020