Home LabaraiA shirye mayakan Boko Haram suke su ajiye makamai – Gaidam

A shirye mayakan Boko Haram suke su ajiye makamai – Gaidam

by Dabo Online
0 comments

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata mai wakiltar Yobe ta gabas, Ibrahim Gaidam, ya bayyana cewa dayawa daga cikin mayakan Boko Haram suna son ajiye makamansu.

Gaidam ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata ganawarshi da ‘yan jarida a birnin tarayya.

Sanatan ya kara da cewa dayawa daga cikin mayakan suna jin tsoron fitowa suce sun ajiye makamansu.

A makon da ya gabata, Sanata ya mika kudurin samar da cibiyar kula da tubabbun mayakan Boko Haram a Najeriya.

Yace; “Babu tantama, dayawa daga cikin ‘yan ta’addar sun tuba, dayawa kuma suna son tuba bisa damarmakin da aka samu. Kungiyoyin zaman kansu dayawa ne suka tabbatar da haka.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00