Home Kiwon LafiyaYanzu yanzu: An samu karin mutane 20 masu dauke da Coronavirus, jumillar 210 a Najeriya

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 20 masu dauke da Coronavirus, jumillar 210 a Najeriya

by Dabo Online
0 comments

Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 20 a daren Juma’a.

Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 210.

“A yau da misalin karfe 10:30 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 20. An samu guda 11 a Lagos, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun da guda 1 a Ondo.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00