Home LabaraiJumillar masu dauke da Kwabid-19 a Kano ya ninka na sauran jihohin Arewa sau 2

Jumillar masu dauke da Kwabid-19 a Kano ya ninka na sauran jihohin Arewa sau 2

by Dabo Online
0 comments

Mutane 21 ne suka kamu da cutar Koronabairas a Kano tun bayan bullarta cikin kasa da mako guda, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da haka.

DABO FM ta tattara cewar adadin wadanda cutar ta kama a jihar Kano sun ninka na sauran jihohin Arewa baki daya.

KAduna da Bauchi suna da 6, Katsina 7, Neja 2.

Haka zalika Kano ta zama jiha ta 4 da tafi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya a bayan jihohin Legas, Ogun da birnin Abuja.

DABO FM ta tattara cewar an fara tabbatar da Koronabairas a jihar Kano ranar 11 ga watan Afrilun 2020.

Tin dai bayan bullar cutar, gwamnan jihar Dr Abdullahi Ganduje ya sanya dokar hana fita a jihar Kano wacce za ta fara aiki ranar 16 ga watan Afrilu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00