Gwamnan jihar Kano, DR Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta sassauta dokar hana fita a jihar.
Gwamnan yace gwamnatin ta dauki matakin ne domin bai wa mutane damar yin siyayyar azumin Ramadan da ya rage saura kwanaki kadan.
“Mutane suna da’a ga dokar tin daga ranar da dokar ta fara. Abu na farko shine dole mu tsare rayukan mutane.”
“Duba da karuwar masu dauke da cutar, ba za mu cire dokar ba a yanzu gaskiya, amma akwai yuwuwar mu sassauta na dan awanni domin mutane suyi siyayyarsu ta azumi.”
“Dole muyi maganar rayukan mutane kafin ayi maganar wani abu daban.”
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake magana da gidan Talabijin na TVC da safiyar yau Laraba.
Haka zalika gwamnan yace tini dai shirin gwamnatin yayi nisa domin fara rabon kayyakin tallafi ga marasa karfi domin rage radadin zaman gida.
Daga karshe gwamnan yayi godiya ga mutanen Kano tare da yin kira da su cigaba da yin da’a ga dokar hana fita domin takaita yaduwar cutar Koronabairas.
Zuwa yanzu dai adadin mutane 73 ne suka kamu da cutar a jihar Kano inda aka samu mutuwar mutum daya.
