Daga cikin hadiman gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, sun fara zubar da hawaye akan Koronabairas neman tallafi.
Hakan na zuba ne a dai dai lokacin da gwamnan jihar ya mika kokon bara ga gwamnatin tarayya domin ta baiwa jihar tallafin Naira biliyan 15 na yakar Koronabairas a jihar Kano.
DABO FM ta tattara cewar babban mai taimakawa gwamnan Kano a harkokin addinai, Ali Baba Agama Lafiya, ya fashe da kuka yayin da yake yin hira a gidan rediyon Express dake Kano a jiya Alhamis.
Kukan ya fara ne a dai dai gabar da ya fara yi wa jihar Kano addu’a sakamakon cutar Koronabairas da ta balle a jihar Kano kamar yadda zaku gani a bidiyon dake kasa.