0
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sassauta dokar hana fita a jihar Kano domin bai wa mutane damar yin siyayyar azumi.
DABO FM ta tattara cewar a ranar 27 ga watan Afrilu, jihar Kano ta shiga dokar hana fita da shugaba Buhari ya sanya ta tsawon mako 2.
Yayin sanar da matakin sassauta dokar ta hana fita, Ganduje ya bayyana ranakun litinin da alhamis, a matsayin ranakun da al’umma domin siyya.
Haka zalika ya bayyana cewar kasuwannin ‘Yankaba da ta Rijiyar Lemo ne kawai gwamnati ta sahalewa budewa da manyan shaguna da suke siyar da kayyakin amfanin yau da kullin.
Sai dai yace za a rika fita ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.
