Home LabaraiMai martaba Sarkin Rano ya rasu

Mai martaba Sarkin Rano ya rasu

by Dabo Online
0 comments

Allah ya yi wa martaba Sarkin Rano, Alhaji Abubakar Tafida Ila rasuwa yau Asabar, 2 ga Afrilun 2020.

Sarkin Rano ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan jihar Kano masu cikakken iko guda 4 da gwamna Ganduje ya samar a shekarar 2019.

Ya rasu ne bayan fama da gajeriya jinya. Tin kafin rasuwarshi rahotanni sun bayyana an aike da shi asibiti domin neman magani.

Mai magana da yawun Masarautar Ranon Wali Ado ya shaidawa BBC cewar; Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti a jiya Juma’a.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00