0
Masarautar Zazzau ta jihar Kaduna, ta karyata rahotannin da aka yadawa cewa ta sanar da ganin sabon watan Shawwal.
DABO FM ta tattara cewar wani limami ne a Zaria, ne ya fitar da sanarwar da sunan Sarkin Zazzau a kan shafinshi na Facebook.
AKan haka ne DABO FM tayi tattaki zuwa masarautar, mun kuma tattauna da jami’in hulda da jama’a na masarautar, Ciroman Shantalin Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan, ya kuma nesanta Sarkin daga fitar da sanarwar.
“Wannan labarin bashi da tushe. Saboda haka, gobe 30 ga watan Ramadana kamar yadda Sarkin Musulmi ya sanar.”
