Jaipur, India (DABO FM) – Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta rika nuna wa ‘yan Najeriya ‘yan ta’addar da yace kullin take ikirarin kashewa.
DABO FM ta tattara tsohon sanatan ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafukanshi na sada zumunta kamar yadda zaku gani a kasa.
Tsohon Sanatan ya ce duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe al’umma, jama’a su na ganin ayyukan ta’addancin da suka yi, a ya yin da bangaren gwamnatin kuma sai dai fitar da rubutun murkushe ‘yan taddar.
“Duk lokacin da ‘yan bindiga suka yi kashe-kashe, muna ganin shaidar ayyukansu na keta da zalunci. Duk lokacin da ku ka (Gwamnati) kashe ‘yan ta’adda, ya na da kyau mu rika ganin iri ayyukanku na bajinta.
A ‘yan kwanakin nan da muke ciki dai, an samu yawaitar hare-haren ‘yan binduga da mayakan Boko Haram a yankunan Arewa maso gabashi da yammacin Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da kisan mutane 81 da mayakan Boko Haram su kayi a jihar Borno, inda hukumar ‘yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane sama da 18 a jihar sakamakon harin ‘yan bindiga.
A nashi bangaren, shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin da mayakan Boko Haram su ka kai garin Borno, sai dai har yanzu ya kasa cewa komai akan hare-haren da ‘yan binduga dadi suke kai wa jihohin Katsina da Sokoto.
