Home Labarai‘In da Jonathan ko wani dan Kudu ne ke mulki, da an ce shirya kashe-kashe ake don cutar Arewa’

‘In da Jonathan ko wani dan Kudu ne ke mulki, da an ce shirya kashe-kashe ake don cutar Arewa’

by Dabo Online
0 comments

Jaipur, India (DABO FM) – Sheikh Jabir Sani Mai Hula, fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, ya magantu kan yadda a ke kisan kiyashi a yankin arewacin Najeriya a ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari.

Cikin wani sako da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook, DABO FM ta tattara yadda malamin ya bayyana zaton da mutane suka yi a shekarar 2015 na cewar “an shirya kashe-kashe domin cutar yankin Arewa.”

Malamin ya ce wannan ikirari sam ba gaskiya bane.

“Duk yadda hasashe ya yi ƙarfi yana iya zama ba gaskiya ba. Da Jonathan ko wani dan kudu ke mulki da mun sha “Billahillazi…” kashe kashe nan kitsa su a ka yi domin a cuci Arewa. Ashe ba gaskiya bane.

“Mu ɗauki darasi a kan yadda mu ke zargin mutane. Allah Ya yafe mana, Ya bai wa shugabanni ƙwarin gwiwar sauke haƙƙin da ke a kansu, Ya kawo mana sauƙi.

A cikin makonnin da muke ciki, rahotanni da dama sun tabbatar da yadda ‘yan bindiga dadi da mayakan Boko Haram suka hallaka mutane kusan 100 a jihohin Borno da Katsina.

Hakan ya jawo da yawa daga cikin al’ummar arewacin Najeriya ke ganin shugaba Muhammadu Buhari ya gaza duba da cewar babban maƙasudin zabarsa shi ne tabbatar da tsaro a Najeriya musamman a Arewaci.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00