1
Wannan na zuwa ne bayan kotu ta tabbatar da Victor Giadom a matsayin shugaban rikon jam’iyyar ta APC bayan jam’iyyar ta bada sunan Sanata Abiola Ajimobi bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatar da Adam Osiomole a matsayin shugaban jam’iyyar a jiya Talata.
DABO FM ta samu rahoton cewa sabon shugaban jam’iyyar ta kasa, Victor Giadom ya soke tantance yan takarar gwamnan jihar ta Edo a safiyar Laraba.
Mr Giadom ya kuma bayyana cewa ya samu goyon bayan kafatanin mambobin kwamitin jam’iyyar. Kamar yadda ChannelsTv ta rawaito.
