Home Labarai‘Rigakafin tsaro ne yasa gwamnatin Kano ta jaddada dokar haramta goyon babur’

‘Rigakafin tsaro ne yasa gwamnatin Kano ta jaddada dokar haramta goyon babur’

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Al’ummar jihar Kano na ta cece-kuce dangane da sabuwar sanarwar da hukumar Karota ta fitar na haramcin goyon babur mai kafa biyu a jihar Kano.

Sai dai dokar ba sabuwa bace, illa iyaka a wannan karon gwamnatin ta ce ta haramta goyon babur din ne a kafatanin jihar Kano maimakon yadda dokar take a baya na iya cikin birnin Kano.

Sakamakon tabarbarewar tsaro a jihohin dake makotaka da jihar Kano, gwamnatin ta ce ya zama tilas ta dauki matakin kare rayukan al’ummar jihar Kano.

A zantawar shugaban kungiyar Karota, Bappa Babba Dan Agundi ya yi da gidan rediyon Arewa, ya ce mutane sun banzatar da dokar wanda a yanzu mutane suna yin goyo iya san ransu a jihar Kano.

Ya kara da cewa duba da yadda ake kai hare-hare a kan babura, ya zamewa gwamnatin Kano dole ta sake jaddada haramcin dokar tare da fadadata zuwa dukkanin fadin jihar Kano.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00