A kokarin su na kubuta daga hare haren ‘yan bindiga, a kalla mutanen kauyukan kananan hukumomi 8 na tara kudi a kowanne wata domin biyan ‘yan bindiga saboda kaucewa harin su.
Rahoton DABO FM ya bayyana yan kauyukan na hadawa ‘yan bindigar naira dubu dari da hamsin kowannane wata domin kubuta daga kawo musu hari kamar yadda wani masanin al’amuran jama’a, Dr. Muttaqha Darma ya tabbatar mana.
Rahoton ya kuma bayyana ‘yan kauyukan da suka gaza biyan irin wadannan kudade tini an fatattake su daga gidajen su da gonakin su.
Kauyukan da abin yafi shafa sun hada da kauyukan karamar hukumar Faskari, kamar Unguwar Tsamiya, Birnin Kogo, Bangi, Kahi, da Raba. Haka kuma wasu ‘yan bindigar na neman kudi a hannun ‘yan kauyukan fiye da 150,000, hakan ya jawo yin hijira ga ‘yan kauyukan.
Da muka tuntubi mai bawa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari shawara a fannin tsaro, Ibrahim Katsina ya bayyana wannan lokutan sun shige, yanzu gwamnati na kokarin maida ‘yan kauyukan da sukayi gudun hijira garin su.
Katsina ya kuma yi kira da mazauna garuruwan da su dinga sanar wa jami’an tsaro da sunga wani abu ba dai dai ba. Kamar yadda KatsinaPost ta fitar.
