Home LabaraiA Gaggauce: Gwamnatin Kano ta cire dokar kulle a fadin jihar Kano baki daya

A Gaggauce: Gwamnatin Kano ta cire dokar kulle a fadin jihar Kano baki daya

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dage dokar kulle a fadin jihar baki daya.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da haka a yau Alhamis yayin wani taro a fadar gwamnatin jihar.

Gwanan ya ce gwamnatin ta yanke shawarar ne bayan samun gagarumar nasara a yaki da cutar Kwabid-19 a fadin jihar Kano.

Kazalika gwamnan ya umarci kafatanin ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aikin daga ranar Litinin mai kamawa.

Sai dai ya yi kira ga mutane da suke da shekaru sama da 55 da su zauna a gidajensu domin su ne mafi kusa da kawuwa da cutar, ya kuma yi kira ga sauran al’ummar jihar Kano da su cigaba da daukar matakan kariya akan cutar.

DABO FM ta tattara cewar zuwa yanzu, ranar Alhamis da karfe 10 na dare, jihar Kano tana da masu dauke da cutar Kwabid-19 kasa da 300.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00