Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sake zaftarewa ma’aikata wani kaso na cikin albashin su duk da yarjejeniyar da kungiyar kwadago tayi da gwamnatin.
Rahoton DABO FM cikin wata hira da ma’aikatan wanda suka nemi a boye sunansu, ma’aikatan sun tabbatar da sake cire musu kaso cikin albashin su na watan Yuni, daya daga cikin su dake kan matakin albashi na 10 ya bayyana an cire masa N9,600.
Da yake bayyana wa manema labarai, wani ma’aikacin yace “Mun sakankan ce muna jiran albashin watan Yuni, abin mamaki sai gani nayi anyi min karfa-karfar N7,600.” Haka wani dake hukumar ilimi shima an zaftare masa N3000 a watan Mayu da Yuli, wanda dama sune karin da ya samu na mafi karancin albashi.
Kwanaki kadan da suke wuce dai kungiyar kwadago karkashin shugaban ta Kwamared Kabiru Ado Minjibir suka cimma matsaya da gwamnatin jihar kan janye yajin aikin jan kunne na kwana 7 da suka shirya biyo bayan zaftare albashin watan da ya gabata na Mayu. Kamar yadda Nigerian Tracker ta rawaito.
