Manzon Allah SAW ya ce: duk wanda yaje wajan boka ko dan tsubbu (mai bada labarin abin da ya wuce ko kuma abinda zai zo nan gaba) allah ba zai karbi sallar sa ba ta kwana 40.
Manzon Allah SAW ya ce : Duk wanda yaje wajan boka mai da’awar yasan gaibu, ya kuma gaskata shi acikin abinda ya bashi labari, hakika ya kafurcewa abinda aka saukarwa Annabi SAW.
Abubuwan da suke kai mutane wajan bokaye;
Na daya, neman wani magani na wata cuta da ta gagara
Na biyu, neman mallakar miji ko mata
Na uku, raba tsakanin masoya ko maaurata. Ko iyaye
Na hudu, neman mulki ko kudi.
Na biyar, korar kishiya ko haukatata.
Na shida, neman miji ko korar aljannu.
Na bakwai, neman a kashe wani ko a haukata shi.
- Boka shine mai da’awar yasan gaibu, ko karya ya keyi ko kuma yana mu’amala da aljannu.
2. Yin sirkulle, da karanta abubuwan da ba a fahimta.
3. Duk wanda yake tsakuda ayoyi da kalasimi
4. Neman a yanka wata dabba ta musamman baka ko fara
5. Ttambayar sunan mahaifiya.
6. Neman wani bangare na jikin mutum, kamar gashi ko farce
7. Neman wani tufafi da mutum ya sanya a jikin sa.
8. Neman kadaita da mutum idan yana cikin jama’a
9. Karanta abubuwan da baa ganewa.
10. Neman aje aga inda kake kwana ko inda kake sanaa.
11. Neman a binne wani abu a gidan. Mutum ko gidan tururuwa, ko kan hanya
12. Rashin yin sallama ko hana yin sallah a gurin sa
13. Hana ka yin wani abu da shari’a ta umarceka na farilla ko wajibi.
Umartar mutum da ya zauna cikin kazanta ko ya karanta wani abu da baya fahimta.
