Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na II, ya bayyana hukunci da ya kamata hukumomi su rika dauka ga wadanda aka samu da laifin fyade.
Sarkin ya bayyana haka ne a wani taron yanar gizo-gizpo da kungiyar MARSV a shirya yau Asabar akan yaki da fyade a NAjeriya
A taron da DABO FM ta kalla, Muhammadu Sunusi ya gindaya wasu hukunce-hukunce da ya kamata ayi doka a kansu domin hukunta masu laifukan fyade.
Sunusi ya ce dole ne a fara mayar da laifin fyade a matsayin laifin ta’addanci. Kazalika hukuncin kar ya tsaya kan kisa kadai.
Tsohon Sarkin yace hukuncin kisa ko dauri ba zai amfanar da yarinyar da aka yi wa fyade ba, don haka ya ce ya kamata malamai su zauna su fitar da kudin fansa da namijin zai biya, kana idan yarinyar tayi rauni, lallai zai dauki nauyin lafiyarta har ta warke kafin a kashe shi.
Haka zalika yayi nuni da cewa sai an canza yadda ake tabbatar da laifin fyade kamar yadda yake a mazahabar Malikiyya, kamar haka;
- Idan yarinyar ta tabbatar da anyi mata fyade.
- Idan wanda ake zargi yua tabbatar da laifinsa.
- Idan tayi ihu, aka hango mutumin ya fita a guje.
- Idan aka tabbatar mutumin da ake zargi ba mutumin kirki bane.
- Idan tabbatar da maniyyi, maziyi da aka samu a jikin matar na mutumin da ake zargi ne
Har yanzu da muke hada wannan rahoto da karfe 1:30 agogon Najeriya, Sarki Muhammadu Sunusi II ya na cigaba da gabatar da bayanai a taron.
–
