Hukumar Kidaya ta Najeriya ‘NPC’ ta yi hasashen cewar za a samu karuwar yara mata da zasu dauki ciki sakamakon rufe makarantu da gwamnatin Najeriya tayi domin yaki da cutar Kwabid-19.
Kazalika hukumar ta ce baya ga daukar cikin, za kuma a samu yawaitar zubar da cikin, wanda hakan zai tilasta barin karatu baki daya ga yara mata.
Shugaban riko na hukumar, Dr Tayo Oyetunji ne ya bayyana haka ranar Asabar a wani taron Kidaya na duniya na shekarar 2020 da birnin Abuja.
Shugaban ya ce an samu karuwar cin zarafi da ake yi wa mata kama daga fyade har zuwa sauran ayyukan cin zarafi ga yara mata.
“Sakamakon rashin zuwa makaranta, yara mata da yawa zasu daina zuwa makarantarma baki daya da kuma sauran illoli da rashin zuwa makarantar zai haifar wanda zai hada da auren wuri, yawaitar daukan ciki, kamuwa da cututtuka da mutuwar masu ciki, masu jego da zubar da ciki.”
Shugaban ya ce cutar Kwabid-19 ta zamewa mata barazana sakamakon takaita musu samun damar zuwa asibiti da ya kamata su rika yi akai-akai.
