Sakamakon rufe makarantu da aka yi a Najeriya, malaman makarantu masu zaman kansu ‘sun shiga halin tausayi, duba da yadda rahotanni suka bayyana cewar ba a biyansu albashi.
DABO FM ta tattara cewar tin dai a watan Maris aka rufe dukkanin makarantu a Najeriya a yunkurin da gwamnatin Najeriya take yi na yaki da cutar Kwabid-19.
“Tabbas malaman makarantu masu zaman kansu suna cikin matsi, na san wadanda suke gararamba a titi ko ciyar da kansu basa iya yi.”
“Dan Allah idan kuna da hali, ku duba malaman makarantu masu zaman da suke kusa da ku, ku taimaka musu. Wannan lokaci ne da ya kamata mu tashi mu taimaki junanmu.
“Yanzu watansu sama da 3 ba a biyasu albashi ba. Ina kira da babbar murya zuwa ga masu makarantu da ku yi wa Allah ku taimaka wa malaman makarantunku domin babu lokacin da ya dace a taimaka musu kamar yanzu.”
