Home SiyasaGanduje bai cancanci zama ko Kansila ba’ – Wike

Ganduje bai cancanci zama ko Kansila ba’ – Wike

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana gwamnan Kano, Dr Ganduje a matsayin wanda bai cancanci rike duk wata kujera ta jagorantar al’umma ba.

DABO FM ta tattara cewar tin dai fara fafutukar yakin neman zaben gwamnan jihar Edo, cece-kuce tsakanin gwamnonin biyu ya kara tsamari musamman kasancewar shugabannin kwamitin yaki neman zaben na jami’iyyar APC da PDP.

Cikin wata ganawa da gwamna Wike ya yi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Ribas dake birnin Porthacourt, ya ce baya ga rashin cancantar Ganduje a jagorancin al’umma, ya zubar da kimar shugaba Muhammadu Buhari.

“Duk inda ake bin tsari, duk da cewa Ganduje yana da kariya (a matsayinsa na Gwamna), bai cancanci sake zama gwamnan jihar Kano ba.”

“Ganduje bai cancani zama dan majalissar tarayya, sanata ko mataimakin gwamna ba, hatta Kansila bai cancanta ya zama ba. Ganin Ganduje yana, magana abin kunya ne ga kasar nan ta Najeriya.”

“Ku kalli yadda ya mayar da nagartar Buhari ta zama abin jayayya da kokwanto, mutumin da ake fada mana bayan daukan sakarci, mutum ne tsayayye kuma kaifi daya da yake jajircewa a kan yaki da rashawa. Dazu ina kallon wani shiri a talabiji ake tambaya, ta yaya Buhari ya je ya fadawa mutanen Kano su zabi Ganduje, mutumin da aka ganshi kuru-kuru yana karbar dala?”

Jami’iyyar APC dai ta nada gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban yaki neman zaben gwamnan jihar Edo, kazalika gwamna Wike yake shugabantar kwamitin yakin neman zaben gwamnan Edo na jami’iyyar PDP.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00