/

‘Abdullahi Abbas zai zama shugaban riko na APC a jihar Kano’

Karatun minti 1

Wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa tsohon shugaban APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas zai zama shugaban riko na jami’iyyar.

Hakan na zuwa ne bayan da uwar jami’iyyar APC ta kasa a yau Talata ta rushe dukkanin shugabancinta a matakin mazabu, kananan hukumomi, jihohi da yankunan Najeriya baki daya a wani taro da ta gabatar wanda ya samu halartar shugaba Buhari.

Kazalika jami’iyyar ta kara wa kwamitin rikon jami’iyyar a matakin kasa wa’adin watanni 6 domin cigaba da rike shugabancin jami’iyyar.

Wata majiya madogariya ta bayyana wa DABO FM cewa tsohon shugaban jami’iyyar  na jihar Kano, “Abdullahi Abbas ne zai sake rike shugabancin jami’yyar a kwamitin riko na wucin-gadi da za a kafa.”

A nata bangaren kuma, jami’iyyar PDP ta yi kira ga hukumar zabe ta INEC da ta soke jami’iyyar APC a Najeriya sakamakon rushe shugabancinta da ta yi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog